Labaran Nishadi

LABARAN NISHADI



LANGUAGES (YARE)

From Chatroom
Hello
Sent By: gluex
Reply


BAFULATANI YAKAI MATARSA ASIBITI...
Wani Bufulatani Ne Ya Kai Matarsa Asibiti, Lokacin Sallar Magrib Yayi, Sai Bufulatani Ya Tafi Yayi Sallah, Kafin Yadawo Sai Aka dauke Wuta Sai Likita Yabi Gado Gado Yana Raba Kandir Damin Su kunna, Bufulatani Ya Dawo Yaga Gadon Kowa Da Wuta Shi Kuma Gadon Matarsa Ba Wuta Sai Yaje Wajen Likita Yace: Naga Ko Ina Da Wuta Amma Gadon Matata Babu, Sai Likita Yace Akwae Na Bewa Kowa Kadir Din, Kaje Ka Tambayi Matarka Mai Yasa Bata Kunna Ba, Yana zuwa Yacewa Matarsa Ina Abunda Likita Yakawo Sai Tace Maigida Rogon Birni? Ai Nima Dakyar Na Cinye, Kuma Abunda Yasa Ban Ajiye Maka Ba, Dan Nasan Ba zaka Iya Ciba, Dan Nima # Dakyar Nacinye
THE END
POST BY: husna

HAJIYA ME CIN CIN
Wata mata ce tana yin cincin na siyarwa amma kullum idan ta tashi sai ta ga babu wani cigaba, ma'ana babu riba ko kadan. Sai ta yanke shawara ta zauna cikin dare ko bera ne yake yi ma ta barna ko zata kama shi. Haka akai kuwa cikin dare kawai sai ta ji ana ta kurmus-kurmus, cikin sauri ta haska fitila kawai sai ta ga mijinta ne yake ta faman tauna, sunahada ido da shi, sai yace: "Na ci na Hamsin"
THE END
POST BY: gluex

DUK BUHARIYYA CE SO KAKEYI MUYI FADA
Wani magidanci ne yana hira da matarsa sai yacemata: Honey gaskiya budurwata Aisha tana qaunata sosai. Matar tace masa, Gaskiya Aisha budurwarka ta burgeni. Maigidan nata yace, Rannan fa har cemin tayi honey na yadace muje Wellcare domin muyi siyayyar kayayyaki. Sai matar tace gaskiya ta burgeni. Sai mai Gidan nata yace, Jiya fa har cemin tayi honey I love u very very much. Sai matar tace masa, Gaskiya budurwarka tana sonka. Sai mai Gidan yace dazu kuwa tacemun, Ina my son (danki)? Kinsan tafiki Qaunarsa. Sai matar tace gaskiya ta burgeni. Qarshe dai sai mai gidan yacemata, Wai ke Sadiya babu abinda yake bata miki rai ne? Budar bakin matar sai tace, Eh babu abinda zance, ai na ganeka: Duk BUHARIYYA ce, So kakeyi muyi fada ka korani gida, Ba inda zani
THE END
POST BY: husna

DAN FULANI JIBRILU A MAKARANTAR KWANA………..HAHAHAHA
Wani yaro ne sunansa jibrilu, aka kai shi makarantar kwana, a gadon dakin kwanan dalibai da ke makarantar da aka kai shi hawa uku ne, sai aka ba shi gado hawa na uku, cikin dare fitsari ya kama shi ya rasa yadda zai yi sai ya fara ihu yana kuka, sai shugaban daliban wannan dakin ya ce waye ya ke mana kuka sai yaron ya ce, Jibrilune daga sama ta uku, gaba daya daliban da ke dakin kwanan suka fara gudu.
THE END
POST BY: husna

NA MANTA TAKALMINA
Wani Bafulatani ne kullum sai an yi masa sata a gonarsa. Abu fa ya dami Bafulatani, sai wata rana ya ce bari na buya ko zan kama barawon. Can kawai sai ga barawo ya zo ya debi amfanin gona ya saba a kafada zai tafi. Sai Bafillace ya kama shi ya ce “Yau dubunka ya shika. Lalle yau akoi lugude a rugga.” Ya tusa keyar barawo suka nufi ruga. Suna cikin tafiya sai barawon ya ce ya manta takalminsa a gona, a saboda haka sai dai su koma su dauko. Sai dan fulani ya ce “Shabbijan, sai da muka jo nan sannan za ka she mu koma gona???” Ya ci gaba da cewa “Ni ba zan koma ba, sai dai ka yi gudu ka je ka dauko ina jiranka” Barawo ya yunkara zai sauke kayan sati don ya koma gona, sai Dan fillo ya ce ” Kai wa ka ke nufin zai maka gadin kayan satarka?? Ai da su za ka je ka dawo, ina jiranka, Wallahi kuma kar ka zauna wasa” Shiru, shiru barawo bai dawo ba, sai Dan fulani ya tafi gida, ya je yana bawa baffansa labari, sai Baffan nasa ya ce, “Amma kai akwai sakarai, maimakon ka she ya tsaya ka je kadauko masa.”
THE END
POST BY: husna



Dou you want to post a story here?
then LOGIN


JOIN ARTISTES COMMUNITY


Download Mp3:- b boy cheling (1) DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Bazan Iya In Manta Dakeba DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Cm Ninja Demo Version DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Cm Ninja Freestyle DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart feat A a son DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Iam Not Ready To Leave U DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Old Lyrics Hot Freestyle DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Zainabul Kubura Full Song DOWNLOAD
Download Mp3:- Trap Freebeat Prod By Music Disaster M_D greathits.wapka.co DOWNLOAD

MEDIA CONTACTS

FACEBOOK
TWITTER
INSTAGRAM

CLICK HERE TO LOGIN OR SIGN UP

BACK TO TOP