Labaran Nishadi

LABARAN NISHADI



LANGUAGES (YARE)

From Chatroom
Hello
Sent By: gluex
Reply


SAFIYA MAI ZARNIN FITSARI……HAHAHA
Wata Budurwace Ta Ari Wayar Saurayinta Tana Game Sai Ta Kamo Wurin Da Ake Aje Sunaye Wato CONTACT tana cikin dubawa tana cin dariya saboda wasu sunaye da ta gani ma abin dariya irin su Khadija mai katon lebo, Aisha mai goshin jirgi, Fati mai faso a kafa, Sadiya mai mai warin baki sai takira wayar shi da wayarta kwatsan sai taga sunanta kamar haka SAFIYA MAI ZARNIN FITSARI.
THE END
POST BY: husna

HAPPY BIRTHDAY BARAWO – INJI BASAKKWACE
Wadansu ’yan fashi ne suka tare mota cike da fasinja suka sa kowa ya kwanta a kan titi. Babban barayin ya ci ado, yana zaune. Sai ya ce yau ba wata sata mai yawa za mu yi ba saboda yau ce ranar haihuwata. Kuma sunana Dauda don haka ko mace ko namiji duk wanda sunansa ya fara da harafin ‘da’ sai ya zo ya fada min sannan ya ce min “Happy Birthday!” Wani Basakkwace na zuwa ya ce sunana Duna. “Happy Birthday barawo!”
THE END
POST BY: husna

MUNA SAYA MISHI (MUNTSAYA MATA)
Wani Inyamiri ne ya halarci zaman kotu sai kuwa ya yi sa’a a ranar ana zaman sauraron karar wata mace da aikata zamba. Da aka kammala sauraron karar sai Alkali ya yanke wa matar hukunci daurin shekaru biyar ko kuma tarar Naira dubu dari biyu da hamsin. Sai Alkali ya yi tambaya da cewa za a tafi da matar gidan kaso amma idan har da akwai wanda zai tsaya mata, to fa za ta iya samun ‘yancinta. Inyamiri ya dubu ya ga babu wanda ya mike ya ce zai tsaya wa matar nan, Sai ya ce a ransa “Hausa mugu ne walayi, zai bari wannan mutum ya yi cekala biyaru a prison saboda tsayawa” Sai ya mike tsaye ya ce “Alkali, Mun saya mishi” Sai Alkali ya ce to tunda an samu wanda zai tsaya mata ba za a kaita gidan kaso ba. Kai kuma ya ya sunanka? Alkali ya tambayi Inyamiri. Inyamiri ya masa da sunanmu ne Chinedu. Sai Alkali ya ce to, za ka biya tarar Naira dubu dari biyu da hamsin don wannan baiwar Allah ta samu ‘yancinta kamar yadda ka fada cewa ka tsaya mata. Chinedu ya ce “Mene ne?” Alkali ya ce Naira dubu dari biyu da hamsin Chinedu ya ce ” Na two hundred and fifty thousand naira be that oo” Alkali ya kwarai Sai Chinedu ya ce “Oga Alkali, mun zauna mishi…kai munkwanta mishi”
THE END
POST BY: husna

WANI MUTUM DA MAHAUKACI
Wanimutum ne yana cikin tafiya, toh dama akwai wani mahaukaci a gabansa sai mahaukacin ya ci karo da naira N1000 sai yayi maza ya dauke. Sai mutumen nan ya ce masa:- “Kai Mallam Bani (ID Card) dina sai mahaukacin Sai mahaukacin ya ce: “hehehe Haba dan Uwa in ni Mahaukacine Ai ni ba Wawa Bane.” Toh idan ID CARD din ka ne Menene Sunanka? Sai mutumin ya ce:-“CENTRAL BANK OF NIGERIA ” Sai mahaukacin ya ce:- “Toh Shekarunka fa?” Sai mutumin ya ce:-‘ “1000” ne. Sai mahaukacin ya ce:-“Lallai Mallam ID CARD dinka ne Amshi,amma ka tabbatar kasa hoton ka nan gaba”
THE END
POST BY: husna

KWADO KO MABUDI?
Wani Bafulatani ne ya je kasuwa wajen da ake sayar da kwadon rufe kofa. Bayan ya yi cinikin kwado daya sai aka miko masa tare da ’yan mabudansa. Bayan ya amsa sai ya cire ’ya’yan mabudan ya sanya aljihu, ya mika wa mutimin kwadon, ya ce: “Ya’yan kawai nake son saye, domin kasuwar da ta wuce na sayi kwadon, ’ya’yansa ne suka fadi, shi ne na ce bari in zo in sayi wasu.”
THE END
POST BY: gluex



Dou you want to post a story here?
then LOGIN


JOIN ARTISTES COMMUNITY


Download Mp3:- b boy cheling (1) DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Bazan Iya In Manta Dakeba DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Cm Ninja Demo Version DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Cm Ninja Freestyle DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart feat A a son DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Iam Not Ready To Leave U DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Old Lyrics Hot Freestyle DOWNLOAD
Download Mp3:- Omar Smart Zainabul Kubura Full Song DOWNLOAD
Download Mp3:- Trap Freebeat Prod By Music Disaster M_D greathits.wapka.co DOWNLOAD

MEDIA CONTACTS

FACEBOOK
TWITTER
INSTAGRAM

CLICK HERE TO LOGIN OR SIGN UP

BACK TO TOP